1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane a Najeriya

June 5, 2020

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa wasu 'yan bindiga dadi sun kashe akalla mutum 21 a wasu kauyuka na jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

Filmstill My Pure Land
Hoto: Bill Kenwright Films

'Yan sanda a Najeriyar sun ce mutanen da ake zargin barayin shanu ne sun fara ne da kisan mutum 15 a wasu kauyuka shida da ke a jihar a ranar Talatar da ta gabata.

Haka nan jami'an sun ce bata-garin sun kashe wasu da ke zaman makoki su shida daga bisani kamar dai yadda kakakin 'yan sandan shiyar, Muhammad Shehu, ya tabbatar.

Yankin arewa maso yammacin na Najeriya dai na fama da hare-hare masu nasaba da rikice-rikice kan iko da filaye da kuma na barayin shanun, inda a wasu lokutan ake ma samun artabu da 'yan banga.

Masana kuma alakanta abin da matsalar sauyin yanayi da kuma karuwar yawan al'uma da ba su da abin yi, hare-haren da suka yi sanadin salwantar mutum akalla dubu takwas cikin tsukin shekaru tara a yanzu, wasu kimanin dubu 200 kuwa suka rasa sukuni.