1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun yi ajalin mutane a Filato da Kebbi

Abdoulaye Mamane Amadou
January 1, 2026

'Yan bindiga sun kai jerin hare-hare a jihohin Kebbi da karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hoto: AP Photo/picture alliance

'Yan bindigar sun shiga kauyen Bum na karamar hukumar Jos ta Kudu dauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi a cikin dare.

Yaushe za a kawo karshen rikicin kabilanci a Filato?

 A  tautaunawar da suka yi da  wakilinmu na jihar Filato Abdullahi Maidawa Kurgwi, babban jami'in hulda da jama'a  na kungiyar raya ci gaban matasan Berom na kasa Rwang Tengwong, ya ce al'ummar yankin sun shiga sabuwar shekara cikin jimami da alhini, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane Tara. Har zuwa wannan lokaci dai babu wata sanarwa daga gwamnatin Filato dangane da afkuwar lamarin

An kai mummunan harin 'yan bindiga a Kebbi

Wasu da harin ta'addanci ya shafa a Najeriya Hoto: Joshua Omiri/AP Photo/picture alliance

Al’ummar kauyukan karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi a Najeriya sun shiga yanayin dimuwa da fargaba, tare da ficewa daga gidajensu, sakamakon harin da ‚yan bindiga a yankin na su, wadanda suka rinka yi wa mutane yankan rago. Wani mazaunin yanzkin ya tabbatarwa wakilinmu Ma’awiyya Abubakar Sadiq yadda mutane kusan 10 suka rasa rayukansu a hannun ‚yan bindigar. 

Najeriya ta kubutar da daliban Kebbi daga hannun yan bindiga
                                                                 
To sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta Kebbi ta ce mutane biyu aka kashe, amma ba takwas ba, kamar yadda kakakin rundunar SP Bashir Usman ya sanar da wakilin namu, ta cikin wani rubataccen sako da ya aike masa. Yana mai karin hasken cewa  jami‘ansu sun bazama cikin kauyukan da lamarin ya faru, don tabbatar da zaman lafiya a ciki. 'Yan bindigar sun shiga karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi a kan babura, daga makwabciyarta jihar Neja, kamar yadda mutanen yankin suka tabbatar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani