1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga sun kashe mutane kusan 20 a Najeriyaa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 21, 2024

Maharan sun bi gida-gida sannan suka fito da mutanen suka harbe su har lahira

Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Hukumomi a jihar Benue da ke tsakiyar tarayyar Najeriya, sun tabbatar da mutuwar mutane 18 sakamakon harin 'yan bindinga a kauyen Mbacher, tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda shugaban karamar hukumar Katsina-Ala Justin Shaku ya sanar.

Karin bayani:An halaka mutane kusan 50 a Benue

Justin Shaku ya ce lamarin ya faru ne a cikin daren Juma'a, bayan da maharan suka bi gida-gida suka fito da mutanen sannan suka tara su wuri guda suka harbe su har lahira, kuma rikici ne na cikin gida.

Karin bayani:Najeriya: Martani kan kisan Fulani makiyaya

Rundunar 'yan sandan Jihar Benue ta bakin mai magana da yawunta Catherine Anene, ta tabatar da faruwar hakan, har ma ta ce sun kaddamar da bincike a kai.

A baya-bayan-nan ne dai gwamnatin jiha ta sanya dokar hana fita a wasu sassanta, sakamakon ta'azzarar fadace-fadace makamantan wannan.