1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutum 17

Abdoulaye Mamane Amadou
May 4, 2021

Wasu jerin tagwayen hare-haren da 'yan bindiga suka kai sun hallaka mutane 17 a jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya mai fama da rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma.

Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Wani mai magana da yawun gwamnatin jihar ya tabbatar wa manema labaran harin, wanda yake zargin fulani makiyaya da aikatawa kan mazauna yankunan Tijime da Achabo da ke gabashin jihar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara.

Ba tun yau ba dai ake samun takun saka tsakanin makiyaya da manoman yankin, tun bayan da gwamnatin jihar ta dauki matakin hana kiwo mai cike da cece-kuce.