'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 10 a Najeriya
August 11, 2026
Wani artabu tsakanin ‘yan bindiga da jami'an tsaron Najeriya ya yi sanadin mutuwar ‘yan sandan kasar 10 a wani yanki da ke Arewacin kasar, wanda rikice-rikice suka dabaibaye, a cewar hukumomi a ranar Talata.
Rikicin, wanda ya faru a ranar Litinin a karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi, ya kuma yi sanadin mutuwar fararen hula biyu da ‘yan bindiga 17, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bashir Usman, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
An kona daruruwan ofisoshin 'yan sanda a yayin rikicin ENDSARS
Usman ya ce ‘maharan sun je wajen ne a kan babura dauke da manyan makamai a lokacin da jami'an tsaro suka tare su.
An gan su ne a kusa da iyakar jihar Zamfara, inda kungiyoyin ‘yan bindiga da ke yawan kai hare-hare kan garuruwa da kauyukan Najeriya suka fi yawa.
'Yan bindiga sun kashe mutane a coci a Najeriya
Kakakin ya kara da cewa wannan abin takaici ne yadda aka rasa hazikan ‘yan sanda 10 a yayin artabun, yayin da wasu biyu suka samu raunuka kuma suke karbar magani.