1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan bindiga sun sace dalibai a Najeriya

August 19, 2021

'Yan sanda a Najeriya, sun ce wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu yara 'yan makarantar Islamiyya su tara a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin kasar.

Nigeria Katsina | Boko Haram-Angriff auf Schule | Freilassung
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Wannan dai wani sabo ne daga cikin jerin sace-sacen jama'a domin neman kudin fansa da ake gani a sassan arewacin Najeriya a yanzu, kamar yadda jami'an tsaron kasar suka tabbatar.

'Yan bindigar cikin jerin gwanon babura ne dai suka kutsa kauyen Sakki da ke a Katsinar, suka kuma yi awon gaba da daliban da ke kan hanyarsu ta komawa gida bayan karatu.

Wasu shaidun sun ce akwai malami guda cikin daliban da aka kwashe.

Runudnar 'yan sanda a jihar ta bakin kakakinta, Gambo Isa, ta ce ana bakin kokari na ganin an kubutar da yaran da ke hannun masu garkuwa da mutanen.