1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yan bindiga sun sace dalibai a Najeriya

May 15, 2026

Yan bindiga dauke da makamai a babura sun sace daliban makaruntun firamare da sakandare a jihar Borno na Najeriya.

Wata makaranta a Arewacin Najeriya
Wata makaranta a Arewacin NajeriyaHoto: Haidar Umar/AFP

Wani mazaunin yankin Ubaidullah Hassan wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan bindigar dauke da muggan makamai a kan babura sun far wa daliban makarantar yankin Mussa a karamar hukumar Askira Uba da misalin karfe 9 na safiyar wannan rana ta Juma'a 15 ga watan Mayun 2026.

Karin bayani:Shekaru 7 da sace 'yan matan Chibok

Kazalika guda daga cikin malaman makarantar ya ce maharan sun tafi da dalibai da dama, duk da cewa akwai wadanda suka ruga zuwa dajin da ke kusa da makarantar. Har ya zuwa wannan lokaci dai da muke kawo muku wannan labari babu kungiyar da ta dauki alhakin sace daliban.

Karin bayani:Najeriya: Karuwar barazanar tsaro a Arewa

A shekara ta 2014, kungiyar Boko Haram ta sace dalibai sama da 270 a makarantar Chibok da ke jihar Borno, wanda ya ja hankalin kasashen duniya. Ta'addanci da sace-sacen jama'a har ma da garkuwa da mutane da ayyukan barayin shanu na daga cikin manyan kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.