1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun sace dalibai a Zamfara

June 4, 2026

Rahotanni daga Najeriya sun yi nuni da cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai bakwai na kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a Kauran Namoda da ke jihar Zamfara.

Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya, Yazid Abubakar ya tabbatar da sace daliban bakwai, inda ya ce an tesa keyarsu zuwa inda ba a san ko ina ne ba.

Karin bayani: Yaushe dalibai za su tsira a Najeriya?

Sai dai guda daga cikin daliban ya samu damar tserewa yayin da ake ci gaba neman sauran, a cewar rundunar 'yan sandan jihar. Sace-sace dalibai a makarantu na ci gaba da jefa fargaba a zukatan jama'ar Najeriya, wanda ya sanya daruruwan malamai suka gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda matsalar tsaro ke kara tinkarar makarantu.

Najeriya musamman yankin Arewa maso yammacinta ta dade tana fuskatar matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.