'Yan bindiga sun sace 'yan makaranta 25 a Najeriya
November 17, 2025
Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane 25 tare da kashe wani ma'aikaci, a wani mummunan hari da suka kaddamar a wata makarantar sakandaren ‘yan mata a arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta ce harin ya auku ne da misalin karfe hudu na asuba a makarantar sakandare ta mata mai suna Government Girls Comprehensive Secondary School da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
Najeriya: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami'a
Harin yazo ne sama da shekara goma bayan sace kusan dalibai mata 300 na Chibok a yankin arewa maso gabashin kasar lamarin da ya jawo suka daga sassan duniya daban-daban.
Har ila yau, 'yan sandan sun ce 'yan bindigan sun rika harbe-harbe domin razana mutane da suke kusa da wajen saboda kar su kai dauki.
Wani jami’in makaranta guda ya rasa ransa, yayin da wani kuma ya ji rauni a lokacin harin na 'yan bindigan.
'Yan matan Chibok: Alhinin cika shekaru 10 da sace su
Yankin arewa maso yammacin Najeriya ya jima yana fama da ta’addanci daga ‘yan bindiga wadanda ke satar shanu da kuma mutane a kauyuka harma da kashe mutane ba gaira ba dalili.