'Yan bindiga sun sako alkalin babbar kotun Kebbi
August 3, 2026
'Yan sandan Najeriya sun sanar da cewa an sako alkalin babbar kotun jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar, wanda wasu mahara suka sace a gidansa mako guda da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Kebbi ta fitar, ta ce an sako alkalin mai shari'a Faruku Hassan Bunza kuma iyalansa da ma'aikatar shari'a ta jihar sun tabbatar da labarin.
'Yan sandan sun ce wadanda suka yi garkuwa da alkalin sun bukaci a biya su kudin fansa, sai dai sun jaddada matsayin hukumomin tsaro na kin amincewa da hakan, amma ba tare da sun yi karin bayani kan yadda aka sako alkalin ba.
Har ila yau 'yan sanda sun ce bayan sakin alkalin a yanzu haka sun kara matsa kaimi domin zakulo wadanda suka shiriya wannan aika-aika don gufarnar da su a gaban hukumomin shari'a.