1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun aikata kashe-kashe a jihar Borno

May 19, 2025

Rahotannin da ke fitowa daga arewa amso gabashin Najeriya, na cewa sabbin hare-haren ta'addanci a karamar hukumar Baga, sun yi ajalin rayukan gommamn fararen hula.

Wani jami'in soja bayan wani hari a garin Baga na jihar Borno
Wani jami'in soja bayan wani hari a garin Baga na jihar Borno Hoto: Pius Utomi/AFP/Getty Images

A Najeriya wasu hare-hare da mayakan Boko Haram suka kai cikin kauyuka biyu da ke karamar hukumar Baga ta jihar Borno, sun yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane 57.

Shaidu sun ce akwai ma wasu sama da mutum 70 din da suka bata, a lamari mafi muni da aka gani a yankin arewa maso gabashin Najeriyar a baya-bayan nan.

Wani da ya tsallake rijiya da baya, Abdulrahman Ibrahim, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Associtaed Press  cewa kungiyar Boko Haram  ta shiga kauyen Mallam Karamti da Kwatandashi, ta tara sama da mutum 100 ta yi cikin daji da su.

Daga bisani ne dai aka tsinci gawarwakin mutum 57 daga cikin su a ranar Asabar.

Mayakan na Boko Haram dai sun zargi mazauna kauyukan ne da kwarmata bayansu ga hukumomi a cewar.