'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar
March 10, 2019![Nigeria Soldaten](https://static.dw.com/image/18566233_800.webp)
Talla
Mayakan na tarzoma sun kai harin ne wani wajen da ake kira Gueskerou da ke cikin yankin na Diffa, inda sojojin a nasu bangaren suka yi nasarar kashe 'yan bindigar 38.
Yankin na makwabtaka da cibiyar Boko Haram da ke a arewa maso gabashin Najeriya. An kuma yi nasarar kwace motoci biyar daga maharan da kuma makamai a cewar ma'aikatar ta tsaro.
A farkon watan Janairun bana, sojojin kasar ta Nijar suka kashe sama da 'yan kungiyar ta Boko Haram 280 a wasu hare-hare da suka kai masu ta sama da kuma kasa. Sabon harin dai shi ne na biyu cikin kasa da wata guda da aka gani a yankin na Diffa.