1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Brazil na martani kan makomar Lula

Abdullahi Tanko Bala
April 5, 2018

Al'ummar kasar Brazil na cigaba da dasa ayar tambaya dangane da makomar tsohon shugaba Luiz Inacio Lula da Silva, bayan da kotun kolin kasar ta yi fatali da karar da ya shigar na kalubalantar hukuncin tafiya gidan yari

Deutschland Berlin Luis Inacio Lula da Silva Ex-Präsident Brasilien
Hoto: Imago/M. Heine

Al'ummar Brazil daga sassa daban ne dai da ma na ketare ke cigaba da yin martani dangane da labarin hukuncin kotun kolin kasar, wanda ya hana shugaba Lula da Silva cimma nasarar kaucewa tafiya gidan yari. 

Akasarin jaridun kasar sun wallafa labarin hukuncin kotun da hotunan tsohon shugaban kasar da sharhuna da ke nuni da cewa kowane lokaci daga yanzu za'a iya jefashi cikin kurkuku.

Bayan mahawara mai zafi na kusan sao'i 11, alkalan kotun kolin biyar daga cikin shida sun nemi ayi fatali ta karar da Da Silva ya shigar na kaucewa zaman gidan yari na shekaru 12 da aka zartar akansa tun da farko. Carmen Lucia, ita ce shugabar kotun kolin.

Zanga zangar dubban 'yan Brazil kan LulaHoto: Getty Images/AFP/M. Schincariol

" Ta ce kamar yadda kuri'ar da muka kada ya nunar, mafi yawanmu a wannan kotu mun yi watsi da wannan roko, wanda ke nuna nasara akan Gilmar Mendes da magistrate Ricardo Lewandowski, da Marcob Aurelio da Celso Mello, wadanda ke neman a amince da wanke shi".

A kofar ginin kotun kolin da ke birnin Sao Paulo dai dubban magoya bayan tsohon shugaban kasar sun yi cincirindo suna rera wakoki suna cewar" sai mun ci nasara a yakin da muke yi a Brazil.

Duk da wannan hukunci da ma sauran zarge zarge da ke kansa, har yanzu tsohon shugaban na Brazil mutum ne mai mutunci a idanun al'ummar kasarsa. Hukuncin kotun ya zo a daidai lokacin da Brazil ke cikin wani yanayi na farfadowa daga halin tsaka mai wuya da ta tsinci kanta na badakalar almubazzaranci da dukiyar kasa da magabanta suka yi ciki harda da da Silva.

Akan haka ne ma ake yin shakku dangane da ko za'a iya tasa keyarsa zuwa kurkuku, ganin cewar farin jinisa a cikin kasar sai karuwa yake yi, kana a daya hannun ya taba kasancewa shugaban kasa. A yanzu haka dai shi ne ke kan gaba a tsakanin dukkan 'yan takarar shugabancin kasar a zaben shugaban kasa da zai gudana a watan Oktoba. Sai dai da wannan hali da ake ciki da wuya a barshi ya yi takara.