1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Burkina na ketarewa zuwa Ghana

February 22, 2023

'Yan Burkina Faso wajen 4,000 ne suka tsere zuwa kasar Ghana domin neman mafaka bayan wani mummunan hari na 'yan ta'adda da ya halaka rayuka.

'Yan gudun hijirar Burkina a Widnaba, Ghana
'Yan gudun hijirar Burkina a Widnaba, GhanaHoto: Maxwell Suuk/DW

Biyo bayan wani hari da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne suka kai wasu yankunan al'ummomin manoma a Burkina Faso, wanda ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama, 'yan Burkina Fason na ci gaba da yin kaura zuwa wasu yankuna a kasar Ghana domin samun mafaka.

Mazauna Ghana da suke kusa da kan iyaka na ci gaba da karbar 'yan gudu hijirar, saboda rashin gina sansanoni ga sabbin 'yan gudun hijirar da hukumomi basu yi ba. Amabile Elisha Afugu mazauniya ce a yankin Widnaba.

 

"Mun dade muna jin labarin  wadannan 'yan Boko Haram da mayakan jihadi a 'yan shekarun da suka wuce a wasu wurare a Najeriya, ba mu yi tsammanin za su zo kusa da mu ba, amma gashi abun ya zo. Matsalar ta faru gare su a yau, ba mamaki gobe ya zo kan mu, ina za mu je? A saboda haka idan yanzu da suka zo idan bamu kyautata musu ba, ranar da abin zai same mu ba zamu san ina za mu je ba."    

Sojoji a Ouagadoudou, Burkina Faso Hoto: Kilaye Bationo/AP Photo/picture alliance

Kamar sauran jama'a da dama, Afugu na ciyar da gomman 'yan gudun hijirar Burkina Faso, amma ba su da kudi da kuma matsugunni na ci gaba da tallafa musu, mazauna yanki sun ce suna bukatar taimakon gwamnati domin ci gaba da ciyar da bakin su.

Amma kamar yadda Stephen Yakubu Minista mai kula da gabashin kasar ta Ghana, ya bayyana, shigowar gwamnati zai kara tsananta kwararar 'yan gudun hijirar ne. 

 

"Abin da muke kokarin kaucewa shi ne, haifar da wani yanayi da zai jawo kwararar 'yan gudun hijira zuwa yankin. Sannan kuma, bama bukatar hakan saboda wadannan mutane ne da suka shigo kai tsaya, suka sage cikin al'umma, jama'a sun shirya karbar su a cikin gidajensu."

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar, Anyanga Anafu ta ce sun ji dadi da suka samu mafaka a Ghana bayyan gujewa tashin hakalin da suka fuskanta a garin su. Anyanga Anafu ta ce:

 

"A kwai jiragen sama masu saukar ungolu na soji da suka rika shawagi a saman gidajen mu. Suna zuwa kullum, amma suna shawagi ne na mintuna biyar kacal. Sannan da daddare kuma, yan ta'addan su zo a motocinsu su yi tafka ta'asa. Ko da za a kashe dubun su a yau, wasu duban za su sake bayyana. Ba za mu iya komawa chan ba."

Masu tafiya gudun hijira a GhanaHoto: Maxwell Suuk/DW

Wasu 'yan kasar sun ce hukumar kare afkuwar bala'o'i ta kasar Ghana suna zuwa ne  kawai domin kirga mutane, wata daya bayan zuwan 'yan gudun hijiran, har yanzu basu samu wani tallafi ba.

Dan abin da ya rage wa iyalan da suke bai wa 'yan Burkina Fason mafaka sun fara kosawa kuma abincin su na iya karewa.