1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan daba sun kai hari kan magoya bayan Peter Obi a Najeriya

November 12, 2026

Harin da 'yan daba suka kai kan magoya bayan Peter Obi da 'yan jarida a Legas ya sake tayar da damuwa kan tsaro da 'yancin gudanar da harkokin siyasa a Najeriya, yayin da ake tunkarar babban zaben kasar.

Tattaunawar DW da Peter Obi, dan siyasar adawa a Najeriya NDC
Tattaunawar DW da Peter Obi, dan siyasar adawa a Najeriya NDCHoto: Musa Tijjani Ahmad/DW

A Najeriya wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan magoya bayan dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar adawa ta NDC, Peter Obi, tare da wasu 'yan jarida a birnin Legas, yayin da ake tunkarar babban zaben kasar.

Rahotanni sun ce maharan dauke da sanduna da adduna da gatura sun kutsa cikin dakin taron magoya bayan Obi, inda suka tarwatsa mahalarta tare da lalata kofofi da gilasan ginin.

Kakakin jam'iyyar NDC, Osa Director, ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da hannu a harin, yana mai cewa ba za su amince da wata barazana da za ta hana su gudanar da harkokin siyasa ba.

Sai dai kakakin jam'iyyar APC, Felix Morka, ya musanta zargin, yana mai bukatar da a gabatar da hujjoji.

Harin na zuwa ne yayin da ake kara nuna damuwa kan tashe-tashen hankulan siyasa gabanin zaben shugaban Najeriya da za a yi a ranar 16 ga watan Janairu.

Edited by:Suleiman Babayo