1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan fafatuka da zaɓen shugaban ƙasar Masar

May 25, 2012

Duk da cewa miliyoyin 'yan Masar sun kaɗa ƙuri'a a zaben shugaban ƙasar, amma ga wasu 'yan fafatuka zaɓe ba na demokraɗiyya ba ne.

Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service An official counts ballots for the presidential election after the polls were closed in the Mediterranean city of Alexandria, 230 km (140 miles) north of Cairo May 24, 2012. Egyptians, choosing their leader freely for the first time in history, voted for a second day on Thursday in an election that is a fruit of last year's popular revolt against Hosni Mubarak. REUTERS/Mohamed Abd El-Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Kimanin 'yan ƙasar Masar su miliyan 50 ne suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen na sabon shugaban ƙasa. To sai dai ba duk 'yan ƙasar ne suka amsa kiran hukumom na kaɗa ƙuri'a ba. Alal misali Engy wata 'yar fafatuka, ta ƙauracewa zaɓen bisa hujjar cewa babu demokraɗiyya da adalci a cikinsa.

Ɗaukacin 'yan ƙasar ta Masar dai sun yi murnar zuwa ranar da suka samu damar zaɓen sabon shugaban ƙasa, amma ban da Engy, mai shekaru 33 'yar juyin juya hali wadda ta taka muhimmiyar rawa

tun a farkon zanga-zangar neman sauyi a dandalin Tahrir. A kan wasu kwalaye da ta manna a bango ɗakinta akwai rubuce rubuce dake adawa da kotunan soji da majalisar mulkin soji. A duk tsawon rayuwarta ba ta taɓa zaɓen shugaban ƙasa ba, kuma a wannan karon ma ba ta kaɗa ƙuri'a ba.

"Ba zan taɓa kaɗa ƙuri'a ƙarƙashin dokokin soja ba. Bayan shekara ɗaya da rabi muna gwagwarmayar neman sauyi, zai yi wuya wanda ya shiga zanga-zangar tun da farkon fari ya yi zaɓe."

Ba a kiyaye dokokin demokraɗiyya ba

Engy ta yi imanin cewa idan ta kaɗa ƙuri'a tamkar amincewa da zaɓen shugaban ƙasar ne da kuma gwamnatin mulkin soji.

A gareta zaɓen bai cike ƙa'idojin demokraɗiyya ba, kasancewa hukumar zaɓen ta ƙunshi magoya bayan tsohon shugaba Hosni Mubarak, inda aka yi watsi da takarar Chairat El-Shater na ƙungiyar 'yan uwa Musulmi da kuma Abu Isma'ila na 'yan Salafiya. Shater ya taɓa zaman kurkuku a lokacin gwamnatin Mubarak sannan Isma'il kuma mahaifiyarsa ta taɓa riƙe fasfo ɗin Amirka. Amma an amince da takarar na hannun damar tsohon shugaban ƙasa duk da dokar majalisar dokoki da ta haramta wa tsoffin muƙarraban gwamnati shiga zaɓen.

Hoto: picture-alliance/dpa

Engy ta yi suka ga abin da ta kira bambamcin sharuɗɗa. Daga cikin 'yan takara 13 mutum ɗaya kaɗai ɗan gwagwarmaya wato Khaled Ali.

"Shin za ka gaya min cewa an gudanar da wannan zaɓen cikin gaskiya da adalci in da aka samu mutane uku ko huɗu 'yan shekaru 70 da suka kashe dubban miliyoyi a yaƙin neman zaɓe, yayin da mu da muka fara juyin juya halin ba mu da ko ƙwandala?"

Wani dalilin da ya hana Engy kaɗa ƙuri'a shine rashin fayyace aikin sabon shugaban ƙasar. Har yanzu ba a sake fasalin kundin tsarin mulki ba, sannan ba a san irin ikon da sabon shugaban da majalisar dokoki da kuma soji za su samu ba.

Ba kowa ne ke da irin ra'ayin Engy ba

Sai dai yayin da Engy ke wannan ƙorafi miliyoyin 'yan Masar ne suka yi cincirindo a rumfunan zaɓe, daga ciki har da Ragab Madbuli wanda ya bayyana muhimmancin wannan rana, kuma ya ce yana alfahari kasancewa a karon farko a rayuwarsa ya samu damar kaɗa ƙuri'a a wani tsabtataccen zaɓe. Ɗan takarar da yake goya wa baya shi ne Ahmed Shafik wanda ya taɓa riƙe muƙamin firaminista a lokacin Hosni Mubarak.

Ahmed ShafikHoto: picture-alliance/dpa

"Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai, na jefa wa Ahmed Shafik ƙuri'a ta domin ya daɗe a fagen siyasa. Yana da ƙwarewa, kuma muna buƙatar gogaggun 'yan siyasa da za su jagoranci wannan ƙasa."

Masu iya magana dai kan ce angulun wani kazar wani. Abin da Ragab ke fata na zaman wani mafalkin abin tsoro ga Engy, wato sake komawar wani sabon Mubarak a kan karagar mulki.

Mawallafa: Viktoria Kleber / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman