Indiya: 'Yan majalisa biyu daga gidan kaso
July 5, 2024Wannan na zuwa ne bayan da mutanen biyu suka samu nasara a zaben da ya gudana cikin watan Yunin da ya gabata, duk da cewa suna tsare a gidan kaso. An dai cafke dan siyasa Amritpal Singh mai shekaru 31 a duniya a bara, bayan jami'an 'yan sanda sun kwashe tsawon wata guda suna farautar sa. Sai dai duk da haka ya samu nasara a zaben, inda ya maka 'yan takara 26 da kasa tare da lashe kujerar majalisa a jihar Punjab. A nasa bangaren Sheikh Abdul "Engineer" Rashid da ya kasance tsohon dan majalisa a yankin Kashmir da ke karkashin Indiya, an cafke shi ne sakamakon zargin da ake masa da daukar nauyin 'yan ta'adda. Sai dai duk da yana tsare, ya lashe zabe a matsabarsa ta Himalaya mai cike da rikici da kuri'u sama da dubu 200. Baki dayan mutanen biyu dai ba a yanke musu hukunci kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba, wanda hakan ya ba su damar tsayawa takara a zaben da suka samu nasarar lashewa.