1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNHR Pakistan Flüchtlinge

September 2, 2010

Rashin kula da 'yan gudun hijiran Pakistan, waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa, zai tilasta musu tsallakawa cikin ƙasar Iran

Waɗanda ambaliya ta shafa a PakistanHoto: AP

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNHCR, ta yi gargaɗin cewa masifar ambaliyar ruwa da ta aukawa ƙasar Pakistan, tana iya tilastawa dubban 'yan gudun hijira tsallakawa izuwa ƙasar Iran.

Lardin Baluchistan dake kudu maso yammacin ƙasar shine ya fara samun matsalar ambaliyar ruwa, wanda ya ɗai-ɗaita Pakistan, inda tun da farko kimanin mutane dubu 200 suka rasa gidajensu a yankin, to amma da ambaliyar ruwan ta yaɗu izuwa wasu sassa na ƙasar, sai aka manta da mutanen yankin, aka yi ta kai agaji ga sabbin wurare da ruwa yaci. An dai samu sauƙin masu daɗa ƙayar baya a wannan lardin wanda shine mafi girma a lardunan Pakistan, kuma shine mafi talauci.

Dama can masu taɗa ƙaysar bayan suna buƙatar gwamnati ta yi raba dai na arzikin ma'adinai da Allah ya baiwa yankin, kuma suna neman ƙwar-ƙwaryan yancin kai daga Islamabad. Don haka ake ganin yin watsi da waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a yankin zai iya kawo tashin hakali, wanda ya lafa shekarun baya.

Mutane da yawa dai sun kamu da cutar amayi da gudawa sakamakon rashin ingantaccen ruwa sha biyo ambaliyar da ta faru, kamar yadda wannan jami'in ke cewa

"Matsalar anan itace, ruwan da ake sha da kuma wuraren yin bahaya, duk sun cakuɗe wuri guda, kai akwai cututtuka da suka caɓe da ruwanda ake sha. Don haka al'ummar yankin ke cikin babbar matsala ta ruwan sha. Kuma hakan yana yaɗa cutar daga wannan zuwa wancan, a tsakanin mutanen"

Wakilin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNHCR a ƙasar Pakistan yace, idan ba'a ɗau matakai na kaiwa mutanen yankin da aka yi watsi das wani ɗauki ba, to basu da zaɓi illa su tsallaka cikin ƙasar Iran.

Wasu daga cikin mutanen da suke sansanonin 'yan gudun hijiran, suna son komawa garuruwansu, to amma babu han'yar mota balle ababen hawa, kamar yadda wannan yake cewa.

"Yanzu ina son komawa gida, amma dole sai nabi cikin ambaliyar ruwa, kuma babu wani kwale-kwale, don haka dole na bi cikin ruwan. Idan na yi sa'a na tararda abun hawa a gaba to, in kuma babu dole da haka zan taka sayyada har gida"

Tantunan 'yan gudun hijiran PakistanHoto: AP

A wannan lardin da ke kudu maso yammacin Pakistan kaɗai, an ƙiyasta aƙalla mutane fiye da dubu 400, suka nemi wurin fakewa, wasu kimanin dubu 600 kuma sun fito daga yankin dake maƙobtaka da su.

Wani jami'in bada agaji mai suna Kebede yace shekaru da dama yana aikin ceto, amma bai taɓa ganin bala'i kamar wanda ya faru a Pakistan ba. Jami'in yace akwai wasu makarantu biyu da ya ziyarta amma baya iya tafiya cikinsu, domin a ɗaukacin yankin ban ɗaki ɗaya ne kacal ake amfani da shi. Don haka Kebede yace yadda ya ga lamarin yankin ya taɓarɓare, kuma babu tallafi dake zuwa, to dole 'yan gudun hijiran Pakistan da na Afganistan, su tsallaka zuwa ƙasar Iran.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu