COVID-19 da marasa galihu a Afirka
April 14, 2020Babu cikakken yanayin kula da lafiya da cakuduwar mutane, kuma annnobar Coronavirus da ke saurin yaduwa ta kara tabarbara al'amura. Tuni masana suka yi gargadi kan irin bala'in da za a fuskanta muddun aka samu barkewar Coronavirus a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Afirka da tasirin da hakan zai yi ga sauran al'umma. An rufe harkokin rayuwa a galibin kasashen, ban da bsngsren sayar da abinci babu abin da yake tafiya.
Dubban 'yan gudun hijira a Yuganda
Kamar yadda wani kiyasi ya Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya nunar, akwai kimanin 'yan gudun hijira milyan daya da dubu 200 a kasar Yuganda, galibi daga Jamhuriyar Dimukuraddiyyar Kwango da Ruwanda da Sudan ta Kudu da kuma Somaliya.#b#
Irin wannan yanayi na da ban tsoro, haka ake ciki tsakanin 'yan gudun hijira a nahiyar daga birnin Maiduguri na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya inda tsagerun Boko Haram masu dauke da makamai ke tayar da hargitsi, zuwa Mali da sauran sassa, kamaryadda dubban mutane suke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab da Kakuma da ke Kenya.
Dakile annobar coronavirus
Patrick Youssef shi ne mataimakin daraktan kungiyar ba da agaji ta Red Cross a nahiyar Afirka, ya ce suna gwagwarmaya domin ganin an dakile annobar Coronavirus a nahiyar. Tuni aka fara neman gwamnatocin manyan kasashe kamar Jamu, su saka hannu domin ba da tallafi. Sannu a hankali dai Coronavirus na yaduwa a Afirka.