1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira da ke sansanin Jamam a Kudancin Sudan na cikin matsanancin hali

July 5, 2012

Kungiyar nan ta 'Doctors Without Borders' da ke bada agaji ta fannin kiwon lafiya ta ce mutanen da ke rasuwa sakamakon cikar da sansanin gudun hijirar ya yi na karuwa matuka.

Hoto: DW

Wata jami'ar kungiyar Tara Newell ta ce galibin mutanen na rasuwa daga cutukan da za a iya magancewa inda ta kara da cewar halin da al'ummar da ke sansanin 'yan gudun hijirar na Jamam wanda ke dauke da mutane sama da dubu arba'in ke ciki na da tada hankali matuka.

Sakamakon wannan yanayin da aka shiga ne ya sanya kusan a kulli yaumin yara tara ke rasuwa a saboda kamuwa da gudawa.

Uwargida Tara ta ce mazauna sansanin galibi na kwana ne kan jikakkun kaya sakamakon ruwan da tafka kamar da bakin kwarya a makon jiya wanda ya yi sanadiyar ruftawar bandakuna tare da bata ruwan sha a sansanin wanda haka ya janyo karuwa zazzabin cizon sauro da ma dai sauran cutuka.

Halin da mutanen da ke sansanin na Jamam su ka shiga dai ya sanya kungiyar ta Doctors Without Borders yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta daukar mataki don ceto rayuwarsu.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman