'Yan gudun Hijira na biyan makudan kudade
January 3, 2015Talla
Bayan da suka isa kasar Turkiya ta jirgin sama daga kasar Lebanon, wadannan 'yan gudun hijira wadanda akasarinsu 'yan kasar Siriya ne, sun shiga cikin wannan babban jirgin ruwa mai suna Ezadeem a ranar 31 ga watan Disamba, a cewar shugaban gundumar Cosenza da ke jihar Calabre a kasar ta Italiya yayin da yake magana a gaban manema labarai. 'Yan gudun hijirar da suka ketara rijiya da baibai, sun ce masu ketarar da su din fuskokinsu a rurrufe, don haka suka samu damar sulalewa daga cikin dumbun jama'a ba tare da an gane su ba cikin jirgin ruwan mai tsawon mita 73 wanda ga ainahi, jirgi ne na suhurin dabobi.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal