'Yan gudun hijira na Yarmuk na cikin halin tsaka mai wuya
April 7, 2015Talla
sanssanni na Yarmuk wanda ke kusa da Siriya a 'yan kwanaki baya-baya nan, ƙungiyoyin tsagairu masu yin jihadi suka riƙa kai wa hare-hare, na fuskantar babbar barazana.
A wani taron manema labarai ta bidiyio da Pierre Krahenbuh wani shugaban wata hukumar ta Majalisar Ɗinkin duniya ta 'yan gudun hijira Falasɗinu UNRWA ya yi, ya ce 'yan gudun hijira kusan dubu 18 'yan falasɗinu suka sarƙe a cikin sanssanin waɗanda ke buƙatar samun ɗauki na gaggawa.