'Yan gudun hijira sun ja hankali a Malta
June 14, 2019Talla
Manyan batutuwa da suka ja hankali a taron na Valleta babban birnin Malta sun hadar da batun samar da aikin yi da batun 'yan gudun hijira da sauyin yanayi. Taron dai ya samu halartar shugabanni daga Faransa da Italiya da Spain da Portugal da Girka da Cyprus da Malta.
Yayin da Spain ke fafutuka ta daga martabarta cikin shugabanci na EU da kuma son ganin EU ta kara inganta dangantakarta da Maroko babban batun dai na zama kokari na hana shigowar bakin haure daga Afirka zuwa Turai. Italiya da Malta na son ganin an tsaurara ga batun ba da mafakar siyasa da tsare-tsaren da suka shafi bakin 'yan gudun hijira. Ga Faransa kuwa batun sauyin yanayi shi ne babban abun da ke gabanta.