1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira a Najeriya sun shiga matsaloli

Al-Amin Suleiman MohammadJune 9, 2016

A Najeriya ‘yan gudun hijira a Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno na kokawa da karancin abinci a watan azumi.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Hoto: Reuters/S.Ini

Yayin da Musulmai ke azumin watan Ramadan dubban ‘yan gudun hijira da suka fito daga sassan Jihar Borno da yanzu haka suka samu mafaka a Maiduguri da jihohin da ke kewayw sun koka kan halin da suke ciki na rashin abinci lamarin da ya fara barazana ga rayukansu.


‘Yan gudun hijira da majalisar dinkin duniya ta tabbtar da cewa sun haura miliyan biyu na gudanar da rayuwa kan tallafin gwamnati da kuma masu ba da taimakon abinci da sutura da kuma magunguna. Sai dai bayanai na nuna cewa a Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da yawancin ‘yan gudun hijira jihar ke zaune ana samun koke-koke kan karancin abinci yayin da ake azumi.

Hoto: DW/Uwaisu Idris


‘Yan gudun hijirar da yawancin su mata ne da kananan yara sun ce suna cikin kunci da rashin abinci. Wani mai suna Madu Mustapha da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Dalori a Maiduguri yayin hira ta wayar tarho ya nuna matsalolin suke ciki a wannan watan na azumi.


Hukumomin na bayyana cewa suna bakin kokari na magance matsalolin ‘yan gudun hijira musamman samar musu da abinci da magunguna da kuma sauran kayayyakin more rayuwa.

Hoto: DW/M. Kindzeka


Yanzu haka dai bayanai sun nuna cewa tallafin da hanshakin dan kasuwar nan Aliko Dangote ya yi alkawarin kai wa ‘yan gudun hijira ya fara isa inda ake sa ran in an raba shi yadda ya kamata zai magance matsalar yunwa da ke addabar ‘yan gudun hijira.