1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Borno: 'Yan gudun sun fara komawa Marte

December 1, 2020

Wasu 'yan gudun hijira kimanin 3,000 sun fara komawa garin Marte mai nisan kilomita 130 daga Maiduguri.

Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Hoto: Government House, Maiduguri, Borno State

Mutanen da suka fara komawa Marte din a Litinin din nan an dauke su a manyan motocin safa-safa daga Maiduguri, inda suka yi zaman hijira na kusan shekaru shida. 

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mutanen sun zabi komawa gida domin gina sabuwar rayuwa. Mutanen na Marte sun dauki matakin ne duk da irin kisan gillar da aka yi wa wasu manoma a Zabarmari a karshen makon da ya gabata. Daya daga cikin 'yan gudun hijirar na Marte Bukar Kyarimi ya ce yana cike da farin cikin komawa mahaifarsa bayan shekaru shida, a yanzu zai je domin gyara gonakinsa da ya kauracewa, kuma yana fata gwamnati za ta samar musu da tsaro.