1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Kamaru da aka manta

Abdourahamane Hassane YB
June 5, 2019

Kamaru na kan gaba a cikin sahun wasu kasashen Afirka dama na duniya wadanda duniyar ta manta da halin da 'yan gudun hijirar kasar suke ciki a sakamakon rikici tsakanin 'yan aware na 'yan Ambazoniya da gwamnati.

Tschad N'Djamena Polizeikontrolle
Jami'an tsaron Chadi ke bincikar 'yan gudun hijira daga Kamaru masu gudun rikiciHoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Yakin basasar da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin na Kamaru da na 'yan awaren na Ambazoniya masu fafutukar kasa a yankin da ake magana da harshen Inglishi ya tilasta wa mutane miliyan daya da rabi ficewa daga matsugunansu a yankin Kudu maso Yammaci da Arewa maso Yammacin Kamaru.

Asibitoci na fuskantar hare-hare mafi muni, yayin da jami'an jinya ke kaurace wa cibiyoyin kula da kiwon lafiya saboda fargabar ka da a sace su ko ma su rasa rayukansu, a halin da ake ciki wasu dubban jama'ar na boye a cikin jeji, ba tare da samun agaji jin kai ba ko kadan da kuma kulawa ta kiwon lafiya, Yara ba sa iya zuwa makaranta saboda an rufe makarantu. Patient Mashariki shi ne shugaban kungiyar NRC me binciken reshen Kamaru a yankin da ake magana da Inglishi, ya ce suna fuskantar cikas wajen kai agaji, ga yara kimanin 780 ba sa zuwa makaranta, asibitoci an kayyade aikinsu musamman a yankunan karkara.

A zahiri dai har yanzu babu wani yunkuri na shirin tattaunawa da wani shirin kai dauki na musamman na agaji daga kasashen duniya. Yayin da 'yan jarida ba sa saka ido sossai a kan tashin hankali don kara matsa kaimi ga sassan biyu da ke fada da juna su daina kai hare-hare a kan farar hula. 

Nan yankin Buea na Kamaru mutane da dama sun ga tashin hankali a cikinsaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Akwai dalilai kamar guda uku dai da cibiyar ta NRC ta Norway take ganin su ne musababin mantawa da 'yan gudun hijira a cikin sahun kasashen da lamarin tashin hankalin ya shafa: Na farko shi ne rashin tallafi na kudade da yadda labarai a game da abin da ke faruwa da kuma sakaci da 'yan siyasa da ke yi wa al'amarin rikon sakainar kashi. Mashariki ya ce duk da haka kungiyoyi na yin kokari sai dai suna fuskantar cikas wajen kai dauki ga al'umma.Ya ce ga dai kungiyoyi da ke son aikin amma babu dama.

A wata ziyara da shugaban cibiyar kula da 'yan gudun hijirar ta Norway Jan Egeland ya kai a Kamaru ya ce irin wannan halayya da kasashen duniya suke da ita na rufe ido a kan abin da ke faruwa a Kamaru ya kamata su daina.
A cikin jerin kasashen da cibiyar ta bayyana wadanda lamarin ya shafa bayan Kamaru, akwai Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Burundi da Ukraine da Venezuela da Mali da Libiya da Habasha da Falasdinu. 

Christoph Hoffmann shi ne kakakin jamiyyar Free Democratic Party (FDP) a Jamus kuma shugaban kwamitin 'yan majalisar dokokin Jamus da ke kula da yankin ya ce "kokarin murkushe masu zanga-zanga a yankin da ke magana da Turancin Ingilishi ba zai cimma nasara ba, a yanzu baki dayan al'umma sun fahimci zama kan teburin sulhu shi ne kadai mafita."