gudun hijirar Siriya sun fi miliyan hudu
July 9, 2015Fiye da al'ummar kasar Siriya miliyan hudu ne ke watse a kasashe makwabta inda suke zama 'yan gudun hijira a yankin, bayan da kasar ta fada yakin basasa. Mutane miliyan daya kuma daga cikin wannan adadi sun fice daga kasar ne watanni goma da suka gabata a cewar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis din nan.
Wannan dai shi ne adadin 'yan gudun hijira mafi yawa a wannan zamani a cewar Antonio Guterres shugaban sashin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce wannan adadi na bukatar tallafin al'ummar kasa da kasa a daidai lokacin da rayuwarsu ke kara shiga wani hali na kaka na ka yi.
Cibiyar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce yadda dubban 'yan gudun hijira ke kwarara zuwa Turkiya ya sanya adadinsu ya kai miliyan hudu da dubu goma sha uku watse cikin kasashe makwabtan Siriya.