1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Yan gudun hijrar Nagorno-Karabakh a Armenia

September 25, 2023

Dubban 'yan gudun hijra 'yan asalin Armenia sun bar Nagorno-Karabakh zuwa Armenia, domin kaurace wa hare-haren dakarun Azerbaijan

Hoto: David Ghahramanyan/REUTERS

Dubban 'yan gudun hijra 'yan asalin Armenia sun bar Nagorno-Karabakh zuwa Armenia. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Azerbaijan Kokarin sasanta Armeniya da Azerbaijan  sanar da karbe iko da yankin kamar yadda hukumomin Yerevan suka sanar.

Tuni dai Armenia ta bude kofofinta ga dubban 'yan gudun hijrar tare da basu masauki, inda take dakon shigowar wasu da suka kaurace wa rikicin Nagorno-Karabakh da ke hannun dakarun  Azerbaijan.

Shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev, ya gana da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda suka tattauna ci gaban da aka samu kan yankin Nagorno-karabakh.