1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Ana ci gaba da tserewa daga Afghanistan

Suleiman Babayo ATB
August 27, 2021

Masu neman tserewa daga Afghanistan tun lokacin da mayakan Taliban suka kwace madafun iko na karuwa a cewar Majalisar Dinkin Duniya fiye da 'yan gudun hijira 500,000 suka tsere daga kasar.

Afghanistan | Pakistan | Grenzübergang in Chaman
Hoto: Saeed Ali Achakzai/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana tsammani fiye da 'yan gudun hijira rabin milyan sun tsere daga kasar Afghanistan tun lokacin da mayakan Taliban suka kwace madafun ikon kasar. A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar kimanin mutane 515,00 za su fice daga kasar zuwa karshen wannan shekara ta 2021. Amma babu tabbacin yadda yanayi zai kasance a cikin kasar saboda rudanin rashin inda aka dosa.

Babu gagarumin dandanzon masu neman fiyewa daga kasar, amma tuni dubban mutane sun fice ta iyakokin kasar ta Afghanistan da kasashen Tajikistan, da Turkmenistan gami da Uzbekistan.