1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan hamayya sun razana masu mulkin Najeriya

Ubale Musa M. Ahiwa
July 7, 2025

A wani abun da ke dada nuna alamun tsoro a bangaren jami‘ai na gwamnatin Najeriya, ana kallon karuwar hari kan ‘ya‘yan sabuwar jam‘iyyar ADC ta masu adawar da suka kafu ba da nufin kalubalantar jam'iyyar APC mai mulki.

Madugun adawar Najeriya, Atiku Abubakar
Madugun adawar Najeriya, Atiku AbubakarHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Duk da cewar dai har ya zuwa yanzun ba su share tsawon mako guda a sabon kawancen ba, daga dukkn alamu jam'iyyar ADC na neman zama kadangaren bakin tulun mahukuntan Najeriya. Kuma kama daga fadar gwamnatin kasar ya zuwa ga ministoci dai, an share karshen mako ana ta ambato da kila ma nunin yatsa bisa ‘ya‘yan sabuwar jam'iyyar ADC.

An dai kai ga ambato rawar wasu a cikinsu yayin da suka yi mulki a baya, wasu kuma aka rika kiran su da masu neman mulki ko ta halin kaka, duka a kokari na dusashe hasken ADC da ke dada nuna alamun tasiri cikin fagen na siyasa. Kuma ko bayan sukar dai, Abujar a wani abun da ke zaman ba sabonba ta ce tana shirin yin gyara a cikin manufar kaiwa ya zuwa wadata ta abinci a daukacin kasar a halin yanzu.

Tsarin na hadaka ne dai ya kai ga masu tsintsiyar bisa mulki, kuma daga dukkan alamu akwai babban tsoron sabuwar hadakar na iya kare ikon na masu tsintsiya a kurkusa. Abdul Aziz Abdul Aziz dai kakaki ne a fadar gwamnatin kasar da kuma yake fadin babu alamun tsoro a bangare na gwamnmatin kasar bisa rawar ADC.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: AFP

Tashin ADC na kama da fatalwa ta siyasa a cikin Tarayyar Najeriyar inda masu tsintsiyar suka rushe jam'iyyun na adawa, amma kuma suke kallon sake tashinsu cikin sunan ADC. Ana ma dai kallon wata sabuwa ta dabarar siyasa inda masu adawar suke fadin suna da imani bisa ADC, amma kuma suna zaman ‘ya‘yan jam'iyyunsu na gado.

Akwai dai tsoron zagon kasa har cikin gidan na tsintsiya a karkashin sabon tsarin da masu siyasar ke kira da sunan Covid 2027. Air Marshal Sadiq Abubakar dai na zaman jigon APC a jihar Bauchi amma kuma ya ce ya kai dauki a cikin jam'iyyar ADC da nufin samun sauyin da ‘yan kasar suke da bukata.

Kokari na gyaran ganga, ko kuma neman a fasa kowa ya rasa; sabon tsarin da ya faro daga tsohon ministar na Abuja dai daga dukka na alamu na iya sauya da dama cikin fagen siyasar Tarayyar Najeriyar a nan gaba. To sai dai kuma tsarin a tunanin Farfesa Kamilu Sani Fagge da ke sharhi cikin batun na siyasa, ya saba da ka'ida ta siyasa a kasar.

Sabuwar guguwar ta siyasa dai daga dukkan alamu na shirin barin baya da kura a cikin Tarayyar Najeriyar inda daukaci na bangarorin biyu dai ke dada nuna alamun ko mutuwa ko kuma yin rai.