'Yan jarida 10 na cikin wadanda suka mutu a Kabul
May 1, 2018Tagwayen hare-hare a birnin Kabul, ya kashe mutane 25 ciki har da dan jarida mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaru na Faransa na AFP Shah Marai, da wasu 'yan jarida guda takwas, kana wani wakilin BBC ya rasa ransa a wani harin na daban a gunduwar Khost da ke gabashin Afganistan din.
Daya daga cikin maharan na Kabul dai ya fake da kasancewa dan jarida, wanda ya bashi damar shiga tsakaninsu kafin ya yi kunar bakin waken. Wannan dai shi ne hari mafi muni da ya ritsa da ma'aikatan kafofin yada labaru tun bayan kifar da gwamnatin Taliban, a cewar kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta Reporters without Border.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya nuna bacin ransa kan harin, wanda kungiyar fafutuka ta IS ta dauki alhakin aiwatarwa.