1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jarida sun lashe kyautar Nobel ta bana

Mohammad Nasiru Awal
October 8, 2021

An karrama 'yan jarida biyu saboda kwazonsu wajen kare 'yancin aikin jarida da ma na fadin albarkacin baki, kamar yadda kwamitin bayar da yabon na Nobel ya fada.

Bildkombo-Die Freidensnobel-Preistraeger Maria Ressa und Dmitry Muratov 2021

An bayyana 'yar jaridar kasar Philippines, Maria Ressa, mai sukar lamirin shugaban Philippine Rodrigo Duterte, da kuma Dmitry Muratov dan kasar Rasha, wanda shi ma ya yi suna wajen sukar shugaban Rasha Vladimir Putin,  a matsayin wadanda suka lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2021.

An karrama 'yan jaridar biyu ne saboda kwazonsu wajen kare 'yancin aikin jarida da ma na fadin albarkacin baki a daidai lokacin da gwamnatoci masu mulkin kama karya ke daukar matakan murkushe masu neman 'yancin walwala da fadin albarkacin baki.

Maria Ressa 'yar shekaru 58 a duniya dai na aiki ne a matsayin shugabar wata jaridar Intanet da ke binciken kwa-kwaf da ake kira Rappler. A shekarar 2020 an yanke mata hukunci bisa laifin cin mutuncin wani ta intanet karkashin dokar kasar yaki da aikata laifuka ta intanet da ake cece kuce kanta, dokar kuma da masu sukar lamiri suka ce an kafata ne don yin "mulkin kama karya a yanar gizo."

Dmitry Muratov: "Karramawa ga jaridar Novaya Gazeta"Hoto: Alexander Zemlianichenko/AP Photo/picture alliance

Shi kuwa Dmitry Muratov na matsayin babban editan jaridar Rasha ta Novaya Gazeta daga 1995 zuwa 2017. Kasancewa ya yi suna wajen aikin jarida na binciken kwa-kwaf a fannin cin hanci da rashawa da manyan laifuka, bakwai daga cikin ma'aikatan jaridar aka yi wa kisan gilla tun daga shekarar 2000.

A martanin da ya mayar bayan jin labarin samun kyautar kamar yadda kamfanin dillancin labarun TASS ya ruwaito, Muratov ya ce "ba shi ya cancanci wannan karramawa ba, karramawa ce ga jaridar Novaya Gazeta. Karramawa ce kuma ga wadanda suka mutu a kokarin kare 'yancin jama'a na fadin albarkacin baki."

Fadar Kremlin na daga cikin na farko da suka taya daya daga cikin masu sukar lamirinta murna tana mai cewa Muratov na aiki ne bisa tunaninsa, yana kuma martaba su. mutum ne mai hazaka, kuma jarumi.

Maria Ressa: "Komai za ka yi ka tabbata kana da hujja"Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Favila

Ita kuma a martanin da ta yi bisa cin kyautar, Ressa ta ce kyautar "ta nuna fili sai da hujjoji abubuwa za su yiwu." A shafinta na Twitter Ressa ta ce duniyar da babu hujja na nufin duniya ce da babu gaskiya da yarda.

Kwamitin bayar da lambar yabon ta Nobel a kasar Norway, ya ce mutanen biyu hazikai ne da suka cancanci karramawa a wannan zamani da aikin jarida da tsarin dimukuradiyya ke fama da matsaloli.

Akalla dai 'yan jaridar za su samu kudaden da za su kai euro dubu 985.