1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar 'yan siyasa ga 'yan jaridar Najeriya

May 3, 2023

'Yan jaridar Najeriya na fama da matsin lamba daga 'yan siyasar kasar da wasunsu ke kallon 'yancin manema labaran a matsayin babbar barazana. Hakan na zuwa ne a yayin da ake bikin ranar 'yan jaridu ta duniya.

Hotan wasu daga cikin jaridun Najeriya
Hotan wasu daga cikin jaridun NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Akalla 'yan jaridu 14 ne dai aka kai wa hari ko kuma aka ci zarafi da musguna musu a lokacin babban zaben da ya shude a Tarayyar ta Najeriya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kasar ke 'yayin' cin tarar kafafen yada labarai, a wani abun da ke kama d zuciyar mai tsumma a bangare na masu mulkin kasar.

Tun kafin zaben na 2023, 'yan jarida 45 ne suka fuskanci hari. Duk da ikirarin mahukunta na kasar na tabbatar da 'yancin a fada ko ba dadi, tana kara fitowa fili; kama daga gwamnoni na jihohi na kasar ya zuwa ga ita kanta gwamnatin tarayya, hakurin 'yan mulki na dada raguwa a kan ayyukan wasu 'yan jaridar kasar.

Dan jarida Haruna Mohammed Salisu da ke wallafa jaridar intanet ta 'Wikki Times' a jihar Bauchi ya shaida wa DW cewa ya ji ba dadi a hannun shugabannin siyasar kasar. 

''Da ma tun tuni gwamnatin jihar Bauchi na nuna rashin jin dadin rahotannin da muke wallafa da ke nuna irin abubuwan da suke yi ba daidai ba. A saboda haka ban yi mamakin kama ni da suka yi a kwanakin baya ba.'' in ji Mohammed Salisu

Sakataren kungiyar 'yan jaridar Najeriya, NUJ, Shuaibu Leman, ya nuna damuwa kan wannan yanayin aiki na 'yan jarida.

''Ana neman musguna wa 'yan jarida kuma hakan zai ci gaba da faruwa har sai an samu dimukuradiyya mai kyau irinta manyan kasashen duniya.'' in ji sakataren na NUJ

Labaran bogi da gaza kai wa ya zuwa kare kai'da ta jaridar dai ya kai ga kara ta'azzara ta kiraye-kirayen neman takunkumi ga masu aikin na jarida a cikin matakan kasar dabam-dabam.