'Yan kasar girka na zanga-zanga kan zabe
July 3, 2015Akalla mutane 25.000 masu ra'ayin a'a a zaben raba gardamar kasar Girka ne suka fito domin zanga-zanga a wannan Jumma'a, yayin daga nasu bangare su kuma masu ra'ayin E su akalla 20.000 suka yi tasu zanga-zanga a birnin Athenes babban birnin kasar ta Girka.
Masu akidar a'a dai shi ne na kin amincewa da matakan da masu bin kasar ta Girka bashi na Tarayyar Turai da Asusun bada Lamuni na Duniya IMF suka gindaya mata, yayin da masu ra'ayin E su kuma ke shirin kada kuri'ar amincewa a zaben rabagardamar da zai gudana a ranar Lahadin nan mai zuwa.
Kasar ta Girka dai na cikin tsaka mai wuya tun bayan kasa biyan kudadan bashin da ake binta, inda ake ganin mai yuyuwa idan masu a'a suka fi rinjaye a zaben, to kasar za ta fice daga gamayyar ta masu amfani da kudin Euro.