'Yan kasar Guinea-Bissau na zaben shugaban kasa
November 23, 2025
A kalla masu kada kuri'a ne 860,000 ne za su zabi gwaninsu a cikin 'yan takara 12 a zaben kasar ta yammacin Afirka da ta fuskanci rikice-rikicen siyasa a baya, ciki har da yunkurin juyin mulki sau da dama. Ana hasashen cewa ta yiwu, shugaban kasar mai ci, Umaro Sissoco Embalo mai shekaru 53 ne ya iya lashe zaben da ake sa ran samun sakamako a hukumance zuwa nan da ranar Alhamis din mako mai zuwa.
Karin bayani:Shugaban Guinea-Bissau ya sanar da ranar yin zaben majalisa
Shugaban zai kara ne da babban abokin hamayyarsa, Fernado Dias da ke samu goyon bayan babbar jam'iyyar adawa ta PAIGC da aka haramta wa shiga zaben. 'Yan kasar na fatan sabon shugabancin ya samar da karin ababen more rayuwa ga 'yan kasa da karin ayyuka domin magance talauci da cin hanci da kuma ta'amulli da miyagun kwayoyi.