1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan Kenya sun yi tir da kashe-kashen da mata ke fuskanta

Mouhamadou Awal Balarabe
January 27, 2024

Alkaluman da gwamnati ta fitar sun nunar da cewar a bara fiye da kashi 30% na mata a Kenya na fuskantar cin zarafi a rayuwarsu, saboda haka ne 'yan kasar suka fantsama kan titunan Nairobi don neman a magance matsalar

Matan Kenya sun fusaka sakamakon kashe-kashen da suke fuskanta
Matan Kenya sun fusaka sakamakon kashe-kashen da suke fuskantaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Daruruwan 'yan Kenya sun gudanar da zanga-zanga a birnin Nairobi don nuna adawa da kisan gillar da aka yi wa mata, sakamakon mutuwar fiye da mata 15 a cikin makonni hudun da suka gabata. Masu zanga-zangar da ke sanye da rigunan da ke dauke da hutunan wadanda aka kashe sun nufi majalisar dokokin kasar, lamarin da ya kawo tsaiko ga cunkoson ababen hawa a tsakiyar birnin Nairobi.

Gwamnati kenya ta nunar da cewar kashe-kashen da cin zarafin mata na karuwa idan aka kwatanta da shekarun bayan. Ita ma kungiyar kare hakkin ta Amnesty International ta ce kisa da mata ke fuskanta daga mazajensu ba abu ne da za a amince da shi ba, inda ta yi kira ga hukumomi da su hanzarta gudanar da bincike da kuma gurfanar da masu laifi gaban kuliya.

 Alkaluman da gwamnati ta fitar a shekarar da ta gabata sun nunar da cewar fiye da 30% na mata a Kenya na fuskantar cin zarafi a rayuwarsu yayin da kashi 13% na fuskantar wani nau'i na fyade.