1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan kodogo za su daka yaji

September 21, 2023

A yayin da wa'adin kungiyar kodagon Najeriya na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ke cika, gwamnatin kasar ta ce tana ta kokarin yin mai yiwuwa da nufin kaucewa yajin da ke iya shafar rayuwa da ma makomar kasar.

Najeriya | NLC | Abuja | Zanga-Zanga | Kungiyar Kodago
Kungiyar kodagon Najeriya, ta saba shirya zanga-zanga ko shiga yajin aikin gama-gariHoto: Uwais/DW

Tuni dai tattaunawa a tsakanin mahukunatan Najeriyar da kungiyoyin kodagon kasar biyu tai tsai wa irin na gwamen jaki, kuma tuni wa'adin 'yan kodagon na tsunduma yajin aikin ya cika. A farkon watan Satumbar nan ne suka bai wa gwamnatin tarayyar karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa'adin makonni uku, na ko dai su biya jerin bukatun da suka hada da daukar matakan rage radadi na zare tallafi ko kuma ma'aikata su zauna a gida har sai hali ya yi. To sai dai kuma daga dukkan alamu 'yan mulkin na ci gaba a cikin karatun gwauro da mari, domin kauce wa yajin da zai zamo karin kumallo a tsakanin 'yan kodagon da sababbin mamallaka Najeriyar. Ministan kodagon Najeriya Simon Lalong dai, ya ce yana da imanin iya shawo kan kungiyoyin kodagon su manta da kokarin daka yajin.

Janye tallafin mai ya sa jama'a cikin kunci

02:58

This browser does not support the video element.

Kungiyoyin kodagon dai na wata ganawa da nufin sanin mataki na gaba, bayan karewar wa'adin ba tare da kai wa ya zuwa samun tallafin mai tasiri ba. Kama daga ma'aikata zuwa ragowar jama'ar cikin gari dai, sannu a hankali al'amura na kara baki sakamakon zare tallafin da ya janyo hauhawa ta farashi da ma jefa da dama a cikin halin babu. Kwamared Deborah Yusuf dai na zaman guda cikin 'yan kodagon Najeriyar da ke fadin in babu tallafi, to kuwa da wuya aiki iya dorewa cikin kasar a nan gaba. In har ma'aikata na karatun wayyo, ita kanta kasuwar dai daga dukkan alamu ba ta tsira cikin rikicin na zare tallafin man fetur din ba. Hauhawar farashi a fadar shugaban kungiyar amintattu ta kananan 'yan kasuwar kasar Kwamared Mohammed Labaran na barazanar rushe jarin 'yan kasuwar kasar.