1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYuganda

Yuganda: Kotu ta kori karar soke dokar 'yan luwadi

Abdourahamane Hassane
April 3, 2024

Kotun tsarin mulkin Yuganda ta yi watsi da daukaka karar da aka shigar kan wata doka da ke hukunta wadanda aka samu da laifi yin luwadi ko madigo.

Hoto: Hajarah Nalwadda/AP Photo/picture alliance

 Wasu wakilai na kungiyoyin kare hakin bil Adama suka shigar da karar domin ganin an soke dokar.Dokar wacce ta tanadi hukuncin kisa ga wadanda aka samu da laifin yin luwadi ko madigo.Shugaba Yoweri Museveni, wanda ke kan mulkin tun a shekara ta 1986, shi ne ya ayyanata a watan Mayun shekara ta 2023.Tun farko Amurka da kungiyar tarayyar Turai da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres sun yi kira da a soketa. To sai dai Museveni,ya ce  babu gudu babu ja da baya a kan dokar.