'Yan majalisa a Aljeriya sun amince da sauyi a kundin mulki
February 7, 2016'Yan majalisa a kasar Aljeriya a ranar Lahadin nan sun amince da wani tsari da zai kai ga samar da sauyi a kundin tsarin mulkin kasar, abin da suka bayyana da cewa zai karawa dimokradiya karfi, sai dai 'yan adawa na cewa wannan abu babu abin da zai haifar na sauyi a kasar.
Cikin abin da wannan sauyi zai shafa dai akwai abin da aka dade ana ta cece-kuce a kansa wato dadewar mulki na shugaba a wannan kasa da ke a Arewacin Afirka, abin da kuma a ke ganin zai bude kofa ne ga mika mulki cikin ruwan sanyi ga shugaba Abdelaziz Bouteflika dan shekaru 78 saboda dalilai na lafiya.
Cikin 'yan majalisar kasar dai da suka amince da wannan tsari 499 sun aminta, yayin da biyu daga cikinsu suka yi rowar kuri'a, 16 basu halarci zaman majalisar ba a cewar Abdulmalek Bensalah firaministan kasar.
A shekarar 2008 an bawa shugaba Boutaeflika dama yayi tazarce a karo na uku sai dai yanzu za a sauya kan wannan tsari inda shugaban kasar shi zai zabi firaminista daga jam'iyya mafi rinjayen kujeru a majalisa.