1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta amince da kawancen tsaro da Koriya ta Arewa

October 25, 2024

Majalisar dokokin kasar Rasha, ta amince yarjejeniyar tsaro a tsakanin kasar da kasar Koriya ta Arewa, abin da ke nufin samar da taimako a tsakanin kasashen a duk lokacin da wani abu na tsaro ya shafi guda.

Putin tare da Kim Jong Un na Koriya ta Arewa
Putin tare da Kim Jong Un na Koriya ta ArewaHoto: GAVRIIL GRIGOROV/AFP/Getty Images

Cikin makon jiya ne dai Shugaba Vladimir Putin na Rashar ya mika takardar bukatar amincewa da hakan ga majalisar kasar.

Kashi 100 ne dai na 'ya majalisar mutum 397 suka amince ba tare da wata hamayya ba, inda yanzu za a mika wa shugaban kasa domin ya sanya hannu.

Dukkanin majalisun dokoki a Rasha dai na matsayin 'yan amshin shatan fadar Kremlin.

Amince wa yarjejeniyar tsaron tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa, ya zo ne bayan Amurka da Koriya ta Kudu sun bayyana cewa akwai shaidun da ke tabbatar da cewa Koriya ta Arewa za ta aika wa Rasha mayaka da za su taimaka mata a yakinta da Ukraine.