An fara sauraron batun tsige Shugaba Jacob Zuma
April 5, 2016Talla
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babbar kotun kasar ta bayyana cewar shugaban ya keta tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar kashe makudan miliyoyin Daloli wajen yiwa gidan sa garambawul.
Jam'iyyar Democratic Alliance ta adawa a kasar ce ta nemi bukatar a tsige shugaba Zuman bayan da kotun kasar ta ce shugaban ya take ka'ida a makon daya gabata.
To sai dai, Shugaba Jacob Zuman na iya tsallake wannan siradin, a yayin da majalisar Dokokin kasar ke bukatar kashi biyu bisa uku na yawan adadin 'yan majalisar gami da goyan bayan jam'iyyar mai mulki a kasar wato ANC da ke cigaba da mara masa baya kafin a kai ga tsige shi.