1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabarbarewar tsaro a yankin Diffa

Mahaman Kanta AMA
April 1, 2019

Majalisar dokokin a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa game da yadda al’amurran tsaro suka kara tabarbarewa a yankin Diffa tare da haddasa mumunar barna na rayukan jama’a

Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

A yayin wata sanarwar da suka fitar ‘yan majalisun dokokin kasar masu wakiltar yankin Diffa sun bukaci gwamnatin kasar musamman ma shugaban kasa  da ya gagauta daukar matakai na kawo saukin ga kuncin rayuwar da jama’a suke fuskanta a yankin Diffa duba da yadda hare-haren Boko Haram suka kara tsawaita a yankin tare da hallaka fararen hula musamman ma mata da kananan yara.

Akalla mutane 40 ne suka mutu soja da farar hula a yankin daga ranar Tara zuwa 26 ga watan Maris na wannan shekarar baya ga garkuwa da mutane musamman ma mata da matasa da kokkona gidajen jama’a, lamarin da ya kara janyo fargaba daga mutane mazauna garuruwan da ke iyaka da Tarayyar Najeriya.

Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

‘yan majalisun dokokin sun bayar da wasu muhimman shawarwari ga gwamnatin daga ciki har da batun sake nisanta ‘yan gudun hijira daga iyakar Najariya da tsawon kilomita 50 don kubutar da sz daga hare-haren Boko Haram

Suma kungiyoyin fararen hula masu fafitukar kare hakin dan Adam sun soki yadda gwamnatin kasar ke kara sakaci zuwa ga kare rayukkan mutanen yankin wadanda tun fil azal ke cikin halin talauci da matsatsi a yayin da su kuma suka nuna fatan kasashen biyu sun kara matsin lanba ga mayakan don kaucewa matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Sai wannan korafin na zuwa ne a daidai lokacin damasana masu fashin baki kan tsaro ke cewa jami’an tsaro na fuskantar matsalolin kayan yaki na zamani.