SiyasaAfirka
'Yan Malawi na zaben sabon shugaban kasa
September 16, 2025
Talla
'Yan kasar Malawi na kada kuri'a a zaben da Shugaba Lazarus Chakwera yake neman wa'adi na biyu na mulkin karin shekaru biyar.
Akwai 'yan takara 17 da suka fafata zaben ciki har da mutumin da shugaban ya gada tsohon Shugaba Peter Mutharika wanda shi ne babban babban mai kalubalantar shugaban.
Zabe cikin matsin tattalin arziki
Ana zaben lokacin da kasar ke cikin matsi na tattalin arziki. Tsohuwar shugabar kasar Joyce Banda tana cikin masu fafatawa a zaben na yau Talata. Zanen ya kunshi na shugaban kasa da 'yan majalisa gami da na kananan hukumomi.
Kasar ta Malawi da ke yankin kudancin Afirka tana da mutane kimanin milyan 21, sannan akwai masu zabe kimanin milyan 7.2, kuma tana cikin kasashe 'yan rabbana ka wadata mu.