1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan matan Najeriya sun kai mataki na gaba

Suleiman Babayo MAB
July 31, 2023

Super Falcons ta Najeriya mai maki biyar ta samun tikitin zuwa zagaye na gaba na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta mata bayan da ta yi (0-0) da Ireland, a birnin Brisbane.A wani ba zata Kwalambiya ta doke Jamus.

Fußball | Afrika-Pokal der Frauen 2022 | Nigeria Super Falcons
Hoto: Tobi Adepoju/Shengolpixs/IMAGO

A gasar neman cin kofin kwallon kafar duniya ta mata da ke gudana a kasashen Ostareliya da New Zealand, Faransa ta doke Brazil da 2 -1, yayin da a wani ba zata Kwalambiya ta doke Jamus da 2-1, kana Japan ta doke Spain da ci 4- 0. Ita kuwa Zambiya ta lallasa Costa Rica da ci 3-1. A halin da ake ciki dai New Zealand wacce ke karbar bakuncin ‘yan wasan FIFA na mata tare da Ostareliya ba za ta je zagaye na biyu ba bayan da Switzerland ta doke ta a wasa mai sosa rai. Amma dai za a dama da Super Falcons ta Najeriya duk da 0-0 da ta yi da Ireland saboda ta samu jimillar maki biyar a wasanni uku.

Vertappen na karyawa inda ba gaba a formule1

Max Verstappen da Sergio Perez bayan kammala tserenFormula1 a Abu DhabiHoto: Kamran Jebreili/AP/picture alliance

A gasar tseren motoci na Formula One, har yanzu Max Verstappen yana ci gaba da jan zarensa bayan lashe gasar da aka gudanar a karshen mako a kasar Beljiyam, inda Sergio Perez ya zo na biyu da tazara mai yawa. Haka ya tabbatar da cewa Verstappen ya samu nasara ke nan makonni takwas a jere inda ya nuna bajinta.

Rikici na ruruwa a hukumar olympics ta Asiya

Kwmitin olympics na Asiya na cikin ruduni sakakon badakalar zabeHoto: Apaydin Alain/ABACA/picture alliance

Hukumar kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta bukaci shugaban hukumar ta Olympica ta Asiya, Randhir Singh dan kasar Indiya ya ci gaba da jagorancin hukumar na rikon kwarta ta yankin  saboda hukumar Olympics ta duniya ta yi watsi da sabon zaben da ya wakana. Tun farko hukumar ta Olympics ta duniya ta dakatar da Sheikh Ahmad Al-Fahad Al-Sabah dan kasar Kuwait na tsawon shekaru uku saboda tsoma baki ta hanyar da ta saba ka'ida inda ya yi tafiya zuwa birnin Bangkok na kasar Thailand gabanin zaben da aka yi a birnin, kuma ake gani matakin ya saba abin da ya dace, a zaben da dan-uwansa Sheikh Talal Fahad Al-Ahmad Al-Sabah ya zama shugaba. Shi ma wanda ya zo na biyu a zaben Husain Al-Musallam ya kasance dan kasar ta Kuwait.

De Grasse na jan zare a tseren mita 200

André de Grasse na Kanada a lokacin wasannin TokyoHoto: ANDREJ ISAKOVIC/AFP

Andre De Grasse wanda ya samu zinare a tseren mita 200 wanda dan kasar Kanada ne ya tsallaka mizanin da ake bukata a shiga wasannin tsalle-tsalle na duniya. Dan shekaru 28 da haihuwa, Andre De Grasse ya samu wannan nasarar a ci gaba da tankade da rairaya na 'yan wasan na Kanada da ke gudana. Ita dai Kanada tana cikin kasashen da suka yi fice a duniya a fagen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

Wani dan tseren keke ya rasa ransa a Amirka

Hatsarin keke na yawan wakana a lokacin tsereHoto: David W. Cerny/REUTERS

A Amirka daya daga cikin matasa masu tasowa da ya kware a fagen tseren keke, Magnus White ya rasa ransa yana da shekaru 17 da haihuwa, sakamakon hadarin da ya samu lokacin da yake koma gida bayan ya kammala samun horo a jihar Colorado da ke kasar ta Amirka. Shi dai Marigayi Magnus White yana shirye-shiryen tafiya gasar da za ta gudana a Scotland cikin wata mai kamawa na Agusta. Marigayin ya taba samun nasara a gasar matasa a tseren keke na Amirka.