1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Najeriya na gaba cikin rasa muhalli

Uwais Abubakar Idris
February 16, 2017

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Mr. Edward Kallon ya bayyana haka da ya ke bayani kan irin mummunan hali na tagayyara da mutane sama da miliyan takwas da matsalar Boko Haram ta shafa a Najeriya.

Nigeria Stadt Borno State
Rayuwa cikin sansanoni marasa inganciHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wakilin na Majalisar Dinkin Duniya da ya kai ziyarar farko a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya tun bayan da ya kama aiki a watan Disamba, ya bayyana irin damuwarsa a kan irin halin da ya iske mata da yara kanana daga cikin mutanen miliyan 14 da rikicin na ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya shafa, inda duk da sansanonin na ‘yan gudun hijira da aka samar fiye da kashi 76 cikin 100 na rakube ne a gidajen ‘yan uwa a yanayin da tattalin arzikin yankin ya shiga mawuyacin hali.

Mr. Kallon ya ce babban kalubale ne da ke fuskantar duniya Najeriya ta zama ta hudu a jerin a matsaloli na  mutanen da suka rasa mahalansu a duniya, wacce ya ce  dole ne cikin watani 18 a kara azama don shawo kan matsalolin in ba haka ba lamarin zai  kara rikirkicewa kasar da ma sauran kasashen duniya.

Ko yaushe zamu koma gida cikin tsaro, shi ne tunanin 'yan gudun hijira a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/EPA/Nigerian Army

Ko da ya ke an samu wadanda suka fara komawa gida, amma jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwar ci gaba da fuskantar kai hare-hare a wasu yankuna.

Mumunan halin da mutanen da suka rasa mahalansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar dai na faruwa a daidai lokacin da ake kiyasin mutane dubu 450 na fuskantar barazanar yunwa nan da watan Disamba mai zuwa.  Wannan ya sanya shirin kadammar da taron kasa da kasa da kasashen Najeriya da Jamus da Norway ke shiryawa don neman tallafi na Dala biliyan daya  ga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniyar ya ce su na da tsari na shekaru biyar da su ke aiki a kai da ya kunshi tsaro zaman lafiya da ci gaba a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, inda suke aiki da majalisar dokoki don kafa hukumar sasantawa da zaman lafiya ga yankin da kwararru suka bayyana za'a dauki shekaru masu dama kafin a kai ga samun daidaituwar al'ammura.