1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban Najeriya sun isa gida daga Ukraine

Uwais Abubakar Idris SB)(ZMA
March 4, 2022

Tawagar farko ta ‘yan Najeriya da suka arce dag yakin kasar Ukraine sun samu sauka a Abuja hedikwatar Najeriya, ‘yan kasar su 475 ne dai suka isa ta jirgin Max Air wanda ya kwaso su daga kasar Romaniya.

Nigeria Abuja | Daliban Nanjeriya daga Ukraine sun isa Abuja
Daliban Najeriya daga UkraineHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

 

Murna dai har baka ga ‘yan Najeriya wadanda mafi yawansu dalibai ne da ma iyayensu da suka tarbi 'yan uwa a filin saukan jiragen sama na Nanmdi Azikiwe da ke Abuja. Sun sauka da kayayyakinsu a yanayi na samun tsira daga yakin da ya rutsa da su a kasar Ukraine din. Shin wane hali suka tsinci kasnu ne a Ukraine? Maryam Ahmed Bashir na cikin wadanda suka samu tsira.

‘'Gaskiya bau sauki amma mun godewa Allah da muka dawo cikin kwanciyar hankali sai dai muna godiya ga gwamnati bisa abinda ta yi mana''

Shi ma dai Saifullahi Usman Dalibi ne da ke karatun aikin likita da ya samu aka kwaso su zuwa Najeriya ya bayyana halin da ya shiga a lokacin da yaki ya barke a Ukraine.

‘'Da yake muna da kungiyar dalibai shi ne muka nemi motoci zuwa kan iyakar Ukraine da Romaniya kafin mu karasa, haka muka yi ta tafiya a kasa kusan sa'o'i shida, nan ma ana ta turmutsitsi ba a bari a shiga, muka sha wahala kafin muka samu muka shiga''

Daliban Nanjeriya daga UkraineHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Akwai dai iyayen yara da suka zo don tarabar yaransu, Mallam Jibril Muhammad ya rungume dansa shin ya yaji a yanzu da yaron ya samu kai wa ga tudun na tsira?

‘'Alhamdulillah kowane hali mutum ya samu kansa sai ya yi godiya, muna cikin murna bisa ga taimakawa da gwamnati ta yi, wadanda suka rage muna fatan su samu a dawo da su gida. Lallai in an samu sulhu yara za su koma''

Mallam Ibrahim Dahiru shi ne jami'in yada labaru na kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air da ya dauko ‘yan Najeriyar ya yi karin haske a kan aikin da suke yi.

Jami'an gwamnatin Najeriya dai sun rubuta sunaye da adireshi na wadanda suka sauka. Ana sa ran saukan wasu karin jirage guda biyu a wannan Jumma'a nan a Abuja dauke da sauran ‘yan Najeriya.