1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Najeriya sun yi satar hanyar jirgin ruwa zuwa Spain

November 29, 2022

Jami'an da ke gudanar da ayyukan ceto a teku sun ce kwanaki 11 wadannan mutane suka kwashe a karkashin jirgin ruwan, inda suka yi ta lilo—kafafuwansu dab da ruwa.

Hoto: Mercedes Menendez/Pacific Press/picture alliance

Wasu 'yan ci-rani sun isa Tsibirin Canary na Spain bayan wata satar hanya ta jirgin ruwa da suka yi. Mutanen su uku da rahotanni ke cewa 'yan asalin jihar Cross Rivers ta Najeriya ne sun hau karkashin jirgin ruwan da ya taso daga Najeriya har zuwa Spain.

Hukumomi dai sun garzaya da 'yan ci-ranin asibiti ganin irin tafiya mai cike da kasada da suka yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin shekarar nan ta 2022 kimanin 'yan ci-rani 15,000 ne suka yi hijira ta barauniyar hanya zuwa Turai, inda ake kiyasin mutum 1,500 daga cikinsu sun rasa rayukansu a sanadiyyar wannan tafiya ta teku mai cike da tsautsayi.