1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Jerin gwanon goyon bayan sojojin Nijar

September 30, 2023

'Yan Nijar mazauna Jamus sun gudanar da jerin gwano a birnin Berlin don nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki tare kuma da jan hankalin hukumomin Jamus kan zagon kasan da suke zargin Faransa da yi wa Nijar.

	
Niger Niamey | Abdourahamane Tiani
'Yan Nijar mazauna Jamus sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya wa sojojin kasar.Hoto: Télé Sahel/AFP

Darurruwan masu jerin gwanon dauke ta tutocin Nijar da kuma alluna, suna rera wakoki na kyamar Faransa sun yi tattaki daga harabar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag i zuwa fadar shugaban gwamnati inda suka yi jawabai kan halin da Nijar ta fada bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli wanda ya kawo karshen gwamnatin Mohamed Bazoum.

Karin bayani: Zanga-zangar korar sojijin Faransa a Nijar

Nassirou Mamadou Watara, daya cikin wadanda suka shirya jerin gwanon ya ce sun mika wa hukumomin Jamus takarku domin ankarar da su kan abin da ke faruwa takamaimai a Nijar, sannan kuma sun ja hankalinsu da su dawo daga rakkiyar Faransa kan takun sakar da take da Nijar tun bayan da sabin jagorin saja suka bukaci da ta fice daga kasar.  

Karin bayani: Jakadan Faransa a Nijar ya fice daga kasar

'Yan Nijar mazauna Jamus sun jaddada amincewarsu da sabuwar gwamnatin mulkin sojan kasar karkashin Janar Abdourahamane Tiani, sannan kuma sun sha alwashin ci gaba da gudanar da irin wannan jerin gwano har sai sun ga abin da hali ya yi a game da takun sakar da Nijar ta shiga da Faransa.