1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

2025: Fatan al'ummar Nijar

Salissou Boukari AH
January 1, 2025

A yayin da shekara ta 2024 ke bana bankwana inda ake shirin shiga sabuwar shekarabta 2025 al'umma maza da mata a Jamhuriyar Nijar na cike da fata iri-iri kama daga batun tsaqro, ilimi, da ci gaban tattalin arziki.

Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Wannan shekara dai da ta yi bankwana ta 2024, shekara ce wadda a cikinta al'umma a Jamhuriyar Nijar ta kasan ce cikin yanayi na kangin rayuwa inda radadin takunkumi da aka kakaba wa kasar ya hadu da matsaloli na rayuwa. Wanda duniya ke fama da shi wanda duk da juriya da al'umma ta nuna mutane sun ji a jikinsu musamman ma dangane da tsadar  rayuwa.

Hoto: AFP/Getty Images

Koma da yake daga bisani hukumomi sun dauki matakai na kawo sassauci a fannin kiwon lafiya, man fetur, da rangwame na siminti sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta haddasa babbar barna a sassa dabam-dabam na kasar. Sai dai kuma al'umar ta Nijar na cike da fata a wannan sabuwar shekara ta  2025.