1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan PDP na ta sauya sheka zuwa APC

Ubale Musa daga AbujaApril 7, 2015

Jam'iyyar PDP da ta share shekaru ta na fadi a ji a Najeriya ta fara rasa 'ya'yanta da suke sauyin sheka ya zuwa ga sabuwar jam'iyyar APC da ke shirin mulkin kasar.

Nigeria - nominierter Präsidentschaftskandidat Muhammadu Buhari und Goodluck Jonathan
Hoto: U. Ekpei/AFP/Getty Images / AP Photo

A wani taron manema labaran da ta kira a cikin gaggawa, PDP ta kira kokari na murde wuya tare da alkawuran karya a bangaren APC domin ta karbi daruruwan 'ya'yan PDP da suke sauya sheka. Kakakin jam'iyyar na kasa Oliseh Metuh ya ce kama-karya ne a tafarki na demokaradiyya a kasar, yadda APC ke karbar 'yan PDP ta na musu tsarki tare da maishesu karbabbu a cikin sabon tsarin nata.

Kama daga Gombe zuwa ga Jigawa da Kebbi dama Edo a yankin Niger Delta sannan da jihar Ondo ta sashen kudu maso yamma, daruruwa na 'ya'yan PDP na baiyyana sabon imaninsu ga sabbabin mamallakan kasar da ke shirin karbar mulki kasa da wattani biyun da ke tafe. Ana dai kallon sabon yanayin a matsayin alamun tsaka mai wuya ga jam'iyyar da ta share shekaru ta na tinkaho a cikin fagen siyasa a Najeriya, yanzu haka kuma ke barazanar fuskantar dogon suma. Hasashen kuma da cewar Alhaji Bashir Maidugu dai na zaman mataimakin mashawarcin PDP ta fannin shari'a, ke zaman mafarkin rana.

Shugaban jam'iyyar PDP bai taimaka wa Jonathan Kai labari baHoto: DW/U.Musa

Ai ba tsarin demokaradiyya ba ne ace jam'iyya daya ce a kasar nan. Wannan ra'ayinka ne. APC ma PDP ce duk wanda suka taka rawar gani in banda Buhari da Tinubu duk 'yan PDP ne. Saboda haka za mu gyara jam'iyyarmu su ma ragowar 'yan APC su dawo muyi aiki tare. Yanzu dai muna ganawa.

Duk da cewar dai har yanzu akwai sauran lale da kila damar tasiri a ragowa na zabukan dai a tunanin Captain Bala Jibrin da ke zaman jigon jam'iyyar APC, sabobbin mammalakan na Abuja ba su shirin bakar aniya ga abokan takun nasu dake shirin jagorantar adawa a kasar.

Inda wata jam'iyyya na shirin kashe wata jam'iyya to da PDP ce ta kashemu. Kuma PDP ta fara tun muna cikin AD da APP suka dauki mukamai suka basu don a daina jin sauran jam'iyyu .Amma dai da yake Allah ba azallumin kowa ba ne ya kawo sauyin da yanzu PDP ta zama abin tausayi”.

Duk da cewar kasar ta najeriya na shirin ci gaba a cikin tsarin na mai karfi sai Allah dai, sabon sauyin da ma tasirin dake shirin mamaye harkoki na siyasar kasar a sakamakonsa dai, a fadar Dr sadiq Abba da ke zaman masani na siyasa ta kasar na shirin kawo sauyin da al'ummar Najeriya suka dauki lokaci suna zaman jiran tsammani a kasa.

Jihihi da dama ne sauyin sheka daga PDP zuwa APC ya shafaHoto: DW/K. Gänsler

Nan da shekaru aru -aru PDP ba za ta mutu ba. Amma dai karfinta zai ragu tasirinta zai ragu, kuma ma abun da ya farun na da kyau a cikin demokaradiyya saboda bai kamata ace jam'iyya daya ce ke mamaye lamura ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani